WASHINGTON, D. C. - Hakan na zuwa ne yayin da tattaunawar tsagaita bude wuta tsakanin Doha da Hamas ke zama cikin yanayi na rashin tabbas.
Ana kyautata zaton wannan mataki na ban mamaki da ya hada da kwace wasu kayan watsa shirye-shirye, hana yada rahotannin tashar da kuma toshe gidajen yanar gizonta, shi ne karo na farko da Isra'ila ta taba yi wa wata kafar yada labarai ta kasashen waje da ke aiki a kasar.
Sa'oi bayan sanar da wannan mataki, an dena jin duniyar tashar ta Al Jazeera a hanyar watsa shirye- shirye na tauraron Dan adam. Ko da yake, shafinsu na yanar gizon da wasu hanyoyin watsa labarai na yanar gizo da yawa suna aiki har ranar Lahadi.
Kamfanin ayyukan nasu ya dade yana watsa rahotanni daga yakin da ake ta yi tsakanin Isra’ila da Hamas, bai kuma tsaya cik ba tun bayan harin da mayakan suka kai kan iyakar a ranar 7 ga watan Oktoba, kuma sun ci gaba da yin aiki ko wacce rana na tsawon sa’o’i 24 a Zirin Gaza, a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a kasa wanda ya yi sanadin mutuwar ma’aikatanta tare da raunata wasu.
Baya ga ba da rahotanni daga cikin yankin na Gaza, Sashen Al Jazeera na Larabci ya kan fitar da bayanan bidiyo na zahiri daga Hamas da sauran kungiyoyin mayaka na yankin.
-AP
Dandalin Mu Tattauna