NIAMEY, NIGER - A wata hirar ta musamman da mai fashin baki kan al’amuran tsaro Abdourahaman Alkassoum ya gargadi gwamnatocin kasashen Yammacin Afrika da su dubi wannan lamari da idon basira don murkushe abinda ya kira babbar barazana.
Abdourahaman Alkassoum ya ce ana iya cewa kasar Mali da riga ta tsunduma akan yadda ‘yan ta’addan suka samu wurin zama sosai suka mamaye ta, kamar yadda Kungiyar IS ita kuma a yankin Sahel ta mamaye bakin iyaka uku na tsakanin kasashen Nijar, Burkina Faso da Malin.
Ya ce kokarin da suke yi yanzu shine na shiga sauran kasashen kewaye salim-alim.
Saurari cikakkiyar hirar su da wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma: