Jami’an tsaro sun yi nasarar cafke mutum hudu da ake zargi da kashe wani yaro mai suna Muhammadu Kabir dan shekara 5 bayan da suka yi garkuwa da shi a jihar Kaduna.
Rahotanni sun ce, daga cikin mutanen da ake tuhuma, har da makwabtan yaron.
Lamarin ya faru ne a yankin unguwar Badarwa da ke jihar ta Kaduna, wacce ke arewa maso yammacin Najeriya.
Rahotanni sun ce ranar Asabar din da ta gabata ne aka nemi Muhammadu aka rasa inda ya shiga, duk da cewa an yi cigiyar shi har a wuraren da ya saba zuwa wasa.
Bayanai sun yi nuni da cewa, daga Kaduna, masu garkuwan sun dauki Muhammadu zuwa Zaria inda daga bisani aka dangana da shi jihar Kano wacce ke da tazarar tafiyar kilomita sama da 200 daga Kaduna.
Shaidu sun ce ba a jima ba, mutanen da suka sace shi suka bugo waya suna neman a biya su naira miliyan 50.
Amma da tafiya ta yi tafiya, an karkare a miliyan biyar, inda suka nemi a ajiye su kusa da gadar Kawo da ke Kaduna kamar yadda rahotanni suka nuna.
Sai dai duk da an biya su kudaden, masu garkuwa da mutanen ba su sako Muhammadu ba.
Bayanai sun yi nuni da cewa, wadanda suka sace yaron sun yi ta wasa da hankalin iyalan Muhammadu.
Amma gabanin a kai ga haka, an ga wani mutum mai suna Galadima tare da yaron a tasha a Kano, inda aka ankarar da mahaifin Muhammadu, amma kafin a kira jami’an tsaro sun bi wata hanyar a cewar rahotanni.
Galidama a unguwar su Muhammadu yake da zama kuma tsohon soja ne, inda bayan da aka kama shi, an tusa keyarsa don ya nuna inda yaron yake.
Rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna ta ce, Galadima da sauran abokan tafiyarsa sun amsa laifin kashe yaron, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Wasu majiyoyi da dama sun ce sun kashe Muhammadun ne, saboda ya gane wasu daga cikin su, domin duk a unguwar ta Badarawa suke a Kaduna.
An tsinci gawar Muhammdu a cikin wani kwalbati a Kano, bayan da Galadima ya raka jami’an tsaro inda suka yasar da shi bayan da suka kashe shi.