Auwalun Daudawa shi ne ya jagoranci ‘yan bindigar da suka sace daliban makarantar sakandaren Kankara ta jihar Katsina, ya kuma gamu da ajalinsa ne da yammacin juma’ar nan, sakamakon wata takaddama tsakaninsa da Tukur Mai Kyalla, wanda shi ma kwamandan wata runduna ce ta ‘yan bindiga a Dajin Gidan Jaja, da ke yankin karamar hukumar hukumar mulki ta Zurmi a jihar Zamfara.
Wata majiya daga dajin na Gidan Jaja, ta shaidawa Muryar Amurka cewa, Daudawa da yaransa sun saci shanun Tukur Mai Kyalla, wanda shi kuma ya ce lalle atabau sai an mayar musa da dabbobinsa.
To sai dai majiyar ta ce “Daudawa ya ki ya mayar da dabbobin na abokan sana’ar tasa, wadanda su kuma suka kai masa takakka, kuma Mai Kyalla ya sami sa’ar harbe Daudawa, inda shi kuma yaran Daudawa suka harbe shi.”
Karin bayani akan: Auwalun Daudawa, Bello Mohammed Matawalle, jihar Zamfara, ‘yan bindiga, Muryar Amurka, Nigeria, da Najeriya.
A cewar wasu rahotannin dai kazamin fada ne ya barke tsakanin gungun biyu na ‘yan bindiga, to sai dai duk da yake babu tabbacin ko rayuka nawa suka salwanta a fadan, to amma dai an tabbatar da mutuwar Daudawa.
Gwamnatin jihar ta Zamfara ma ta tabbatar aukuwar wannan lamarin, ta bakin kwamishinan lamurran tsaro Abubakar Dauran, wanda ya bayyana yakinin cewa “alhakin rantsuwa ne ya rutsa da Auwalun Daudawa.”
Saurari Kwamishinan Lamurran Tsaro na Jihar Zamfara, Abubakar Dauran.
A watan Satumban da ya gabata ne dai Daudawa ya bayyana cewa ya tuba daga ayukan ta’addanci, a karkashin shirin sulhu na gwamnatin jihar.
Daudawa ya jagoranci wasu yaransa, ciki har da wasu mutane 6 da aka kai harin makarantar Kankara tare da su, inda suka mika makamansu, bindigogin AK-47 akalla 20, da RPG (bindiga mai jigida) daya, a wani bikin tuban su da aka yi a fadar gwamnatin jihar Zamfara.
Auwalun Daudawa da yaran na sa, sun yi rantsuwa da Alkur’ani a wajen taron, cewa ba za su sake komawa sana’ar ta sata da kisan mutane ba.
To sai dai Daudawa ya ta da tubarsa, inda bayan ‘yan watanni ya koma daji ya ci gaba da sana’arsa, kafin dubunsa ta cika.
Lamarin na Daudawa dai ya kara saka ayar tambaya a shirin na sulhu da ‘yan bindiga da gwamnan jihar ta Zamfara, Bello Mohammed Matawalle ya dage akai, musamman daga bangaren wadanda tun farko suke kalubalantar shirin sulhun.