Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Nuna Takaicinsa Kan Yadda Gwamna Ortom Yake Yin Zarge-Zarge A kansa


Buhari (hagu) Samuel Ortom (dama) (Instagram Buhari/Ortom)
Buhari (hagu) Samuel Ortom (dama) (Instagram Buhari/Ortom)

“Akwai bukatar Benue ta hada kai da gwamnatin tarayya, don aiwatar da  wasu tsare-tsare da aka shimfida don magance matsalar tsaro da ke barazana ga zaman lafiya da ci gaba.” In ji fadar shugaban kasa.

Fadar gwamnatin Najeriya ta mayarwa da Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom martani, kan abin da ta kira zarge-zarge da gwamnan ke yi akan Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatinsa.

Cikin wata sanarwa da kakakin Buhari Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Juma’a, fadar shugaban kasar ta nuna takaicinta kan yadda gwamna Ortom ke yawan zargin shugaban kasar.

Jihar ta Benue a farkon makon nan, ta fuskanci wasu hare-hare wadanda suka yi sanadin mutuwar wasu mutane, lamarin da ya sa gwamna Ortom ya nuna gazawar gwamnatin tarayya wajen daukan matakan kare rayukan al’uma.

“Ina mai cike da takaici da bakin cikin jin cewa, gwamnan jihar Benue Samuel Ortom, na yin zarge-zarge a kaina da gwamnatita, bayan hare-haren da aka kai a jihar.”

Karin bayani akan: Samuel Ortom, jihar Benue, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Sanarwar ta Malam Garba Shehu, wacce ke dauke da sakon jaje ga al’umar jihar ta Benue dangane da wadannan hare-hare, ta ce akwai bukatar gwamnatin Samuel Ortom ta hada kai da tarayya.

“Akwai bukatar Benue ta hada kai da gwamnatin tarayya, don aiwatar da wasu tsare-tsare da aka shimfida don magance matsalar tsaro da ke barazana ga zaman lafiya da ci gaba.”

“Za a iya yin hakan, idan aka saka bukatun mutane a farko sama da wasu bukatu na daban. Kamata ya yi, gwamnatin da jama’a ta zaba, ta rika kallon jama’ar a matsayin ubannin gida ba bayi ba.” In ji sanarwar Garba Shehu.

Amma Ortom ya yi ikirarin cewa ya sha jan hankalin gwamnatin tarayyar kan matsalar tsaro da ta addabi jihar, ba tare da an dauki wani mataki ba.

Akalla mutum bakwai aka kashe a wani sansanin ‘yan gudun hijira a Makurdi a ranar Talata, lamarin da ya fusata matasa suka fara zanga-zanga akan titunan birnin.

Gwamna Samuel Ortom kan dora alhakin ire-iren wadannan hare-hare ne akan Fulani, wadanda yake zargi da ta da fitina a jiharsa wacce ke tsakiyar arewacin Najeriya.

A karshen watan Maris, Ortom ya tsallake rijiya da baya, bayan da wasu ‘yan bindiga wadanda ya ce Fulani ne, suka kai mai hari a lokacin yana rangadin gonarsa da ke wajen birnin Makurdi.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG