Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DSS Ta Kama Dr. Usman Bugaje


Dr. Usman Bugaje (Instagram/Usmanbugaje)
Dr. Usman Bugaje (Instagram/Usmanbugaje)

Bayanai sun yi nuni da cewa tun da misalin karfe 10 na safiyar ranar Laraba, aka kama Bugaje.

Rahotanni daga Najeriya na cewa, hukumar tsaron farin kaya ta DSS, ta kama fitaccen dan siyasar nan Dr. Usman Bugaje.

An kama Dr. Bugaje ne bayan ya kammala tsokaci a wani shirin gidan talbijin na AIT, inda ya nuna gazarwar gwamnati a fannin samar da tsaro a kasar.

Wata majiya kwakkwara daga iyalan tsohon dan majalisar wakilan, ta tabbatar wa da Muryar Amurka aukuwar wannan lamari.

Bayanai sun yi nuni da cewa tun da misalin karfe 10 na safiyar ranar Laraba, aka kama Bugaje.

Karin bayani akan: Dr. Usman Bugaje, Boko Haram, Shugaba Muhammadu Buhari, Muryar Amurka, Nigeria, da Najeriya.

An kuma tsare shi ne har na tsawon sa’a 8 a ofishin hukumar, amma daga baya aka sake shi.

Bincike ya nuna cewa Dr. Usman Bugaje ya nuna damuwarsa ne kan yadda matsalar tsaro ta kara ta’azzara a Najeriya a hirar da aka yi da shi.

Kokarin jin ta bakin hukumar ta DSS ya cutura.

Wannan ba shi ne karon farko da Bugaje, yake caccakar gwamnatin Muhammadu Buhari ba, ko a baya ya taba sukar gwamnati kan yadda tattalin arzikin kasar ke fuskantar koma baya.

Hakazalika, wannan ba shi ne karon farko da hukumar ta DSS take tsare fitattun mutane musamman na bangaren adawa ba, idan suka yi wani tsokaci da ya danganci na sukar gwamnti.

XS
SM
MD
LG