Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Sojan Najeriya Ya Duro Daga Jirgin Sama Bayan Da ‘Yan bindiga Suka Kakkabo Jirginsa


Flight Lieutenant Abayomi Dairo, a Tsakiya
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:15 0:00

Flight Lieutenant Abayomi Dairo, a Tsakiya

Bayan da ya duro daga jirgin, Dairo ya yi amfani ne da duhun dare ya yi ta kaucewa tungar maharan da ke cikin dajin har ya kai sansanin sojoji, inda daga karshe aka cece shi.  

Rundunar sojin sama ta Najeriya, ta ce wani sojanta ya kubuta bayan da ‘yan bindiga suka budewa jirgin da yake ciki wuta yayin da yake aikin yakar ‘yan fashin daji.

Wata sanarwa da kakakin rundunar ta Air Commodore Edward Gabkwet ya fitar a ranar Litinin, ta ce ‘yan bindiga sun budewa jirgin Flight Lieutenant Abayomi Dairo a daidai kan iyakar Zamfara da Kaduna lamarin da ya sa jirgin fado kasa.

“Sai dai an yi sa’a’, jarumin matukin jirgin Flight Lieutenant Abayomi Dairo ya fice daga jirgin.

“Ya yi amfani da dabarun yakin da ya sani, ya kaucewa fadawa hannun ‘yan bindigar, ya nemi mafaka a wani wuri ya jira gari ya waye.” A cewar Gabkwet.

Karin bayani akan: Air Commodore Edward Gabkwet, sojoji, Zamfara, Nigeria, da Najeriya.

Sanarwar ta kara da cewa, Dairo ya yi amfani ne da duhun dare ya yi ta kaucewa tungar maharan da ke cikin dajin har ya kai sansanin sojoji, inda daga karshe aka cece shi.

A cewar Gabkwet, jirgin na faduwa, babban hafsan sojin saman Najeriya Air Marshal Oladayo Amao, ya ba da umarni a yi duk abin da za a yi don ceto ran matukin jirgin.

“An tura dakaru na musamman da sojojin kasa na Najeriya, wadanda suka gano inda jirgin ya fadi da kuma kumbon da ya yi amfani da shi ya duro daga jirgin, yayin da kuma wasu suka bazu cikin dazukan da ke kusa don neman matukin.”

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce, duk da faduwar da jirginta ya yi, “ta himmatu wajen ganin sun cin ma kudurin shugaban kasa da nauyin da kundin tsarin mulki kasa ya dora a wuyansu.

Wannan lamari ya faru a daidai lokacin da hukumomin Najeriya suka bayyana cewa sun yi cefanan wasu jiragen yaki na sama.

Dakarun na Najeriya na yaki ne da ‘yan fashin daji da suka addabi arewa maso yammacin kasar, a wani mataki da gwamnati take dauka na kawo karshen hare-haren da suke kaiwa tare da sace mutane don neman kudin fansa.

Mutanen Da ‘Yan Bindiga Suka Kashe

Mutanen Da ‘Yan Bindiga Suka Kashe
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:20 0:00

XS
SM
MD
LG