Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Shugaba Ghani Ya Fice Daga Kabul Bayan Isar Mayakan Taliban


Ashraf Ghani
Ashraf Ghani

Sai dai Abdullah Abdullah, wanda shi ke jagorantar majalisar sasantawa a kasar, ya wallafa wani sakon bidiyo a Facebook, yana sukar Ghani. 

Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani tare da mataimakinsa da sauren manyan kusoshin gwamnati sun fice daga kasar a ranar Lahadi, lamarin da ya ba mayakan kungiyar Taliban damar sake karbe mulki shekara 20 bayan da dakarun Amurka suka kawar da su.

Ba a dai ji wasu kalamai daga Ghani ba. Amma a wani jawabi da aka nada a ranar Asabar, Ghani ya fadawa al’umar kasar cewa yana kan tuntubar masu ruwa da tsaki na cikin gida da waje kan lamarin, wanda ya kwatanta a matsayin “mamayar yaki.”

Sai dai Abdullah Abdullah, wanda shi ke jagorantar majalisar sasantawa a kasar, ya wallafa wani sakon bidiyo a Facebook, yana sukar Ghani.

“Ina ga tsohon shugaban kasar ya bar kasar cikin mummunan yanayi, Allah zai tambaye shi.” Abdulllah wanda ya tabbatar da ficewa Ghani daga kasar ya fada.

A halin da ake ciki, babu dai wanda ya san inda Ghani yake

Mataimakin shugaban kasar Amrullah Saleh, wanda aka ce shi ma ya fice daga kasar, ya wallafa a shafin Twitter cewa, ba za su mika wuya ga Taliban ba, amma kuma bai ce uffan ba kan rahotanni da suka ce shi ma ya fice daga kasar.

Kungiyar Taliban ta karbe ikon mafi akasarin yankunan kasar cikin mako guda, ta kuma kai kofar shiga birnin Kabul a ranar Asabar.

Mayakan Taliban
Mayakan Taliban

Sai dai mayakan tsagerun sun tsaya a wajen gari, inda suke fadin cewa suna son a “mika mulki cikin ruwan sanyi” saboda a kaucewa tsunduma birnin cikin rikici.

Da safiyar ranar Lahadi, wata tawagar Taliban ta yi zaman tattaunawa da shugabannin jihadi, ‘yan siyasa, da dattawa, zaman da ya kai ga Ghani ya ajiye mulkin ya fice, kamar yadda wasu majiyoyi da ke da masaniya kan lamarin suka fadawa VOA.

A zaman tattaunawar, kungiyar ta Taliban ta ce ba za ta yi zaman mika mulki tsakaninta ta Ghani ba, tana mai cewa dama shi “haramtaccen” shugaba ne.

Mai magana da yawun Taliban Suhail Shaheen, wanda na daya daga cikin tawagar kungiyar da ke ofishinta a Doha, ya fada cikin wata sanarwa cewa an ba mayakan kungiyar umarnin kada su cutar da kowa ko su kai har kan gwamnati ko wani wuri na masu zaman kansu a lokacin da mayakan suka doshi yankin.

Mai magana da yawun Taliban Suhail Shaheen
Mai magana da yawun Taliban Suhail Shaheen

“Duk wanda aka samu da laifi, zai fuskanci fushin hukuma daga Taliban.” Shaheen ya ce yana mai jaddada cewa, “suna so ne a mika mulki cikin lumana.”

Kakakin kungiyar har ila yau ya tabbatar a ranar Lahadi cewa, an ba mayakansu umarnin su shiga wasu yankunan Kabul domin samar da tsaro “don a kaucewa ta da husuma da wawure kayan jama’a bayan ficewa dakarun kasar.

Yadda kungiyar ta Taliban ta kai mamayar cikin sauri ya shammaci mutanen kasar da kuma kasashen duniya. Duk da cewa an ga karin tashe-tashen hankula a bara, bayan da Taliban ta rattaba hannu da Amurka, wannan yunkuri na baya-bayan akan biranen kasar ya zo wa mutanen da mamaki.

Zuwan Taliban kofar birnin Kabul ya sa ofisoshin jakadancin kasashe da dama cikin hanzarin kwashe jami’ansu.

Wani girgin yakin Amurka yana shawagi a kusa da ofisin jakadancin Amurka a Kabul
Wani girgin yakin Amurka yana shawagi a kusa da ofisin jakadancin Amurka a Kabul

Amurka na shirin tura dakaru 1,000 gami da 3,000 da aka ba su umarni a makon da ya gabata, don su taimaka wajen kwashe jami’an diflomasiyyar kasar. An ga jirage masu saukar ungulu suna jigilar jami’an zuwa filin tashin jirage na Kabul.

“Mun fadawa wakilan Taliban a Doha cewa, duk wani mataki da suka dauka a Afghanistan, wanda ya jefa wani jami’inmu cikin hadari ko wani aiki da muke yi, zai gamu da martaninmu ba tare da bata lokaci ba.” Shugaban Amurka Joe Biden ya fada a cewar wata sanarwa da Fadar White House ta fitar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG