A Afghanistan a jiya Lahadi, wadanda wasu hare-hare suka shafa da shaidun gani da ido sun fada wa kamfanin dillancin labaran Associated Press cewa hare-hare ta sama da gwamnati ta kai a yankin arewacin kasar sun yi sanadiyyar kisan akalla mutane 24, ciki har da yara, tare da raunata wasu su shida.
Wasu da suka shaida lamarin su biyu da kamfanin dillacin labaran na Associated Press ya tuntuba, sun ce galibin wadanda aka kashe a hare-haren da aka kai a ranar Asabar, da suka shafi kauyen Sayed Ramazan a lardin Kunduz, farar hula ne.
Hare-haren ta sama na zuwa ne yayin da wakilai da ke shawarwari daga bangaren gwamnati da ‘yan Taliban ke ganawa a karon farko a Qatar don kawo karshen yaki da rikice-rikicen da aka kwashe shekara da shekaru ana yi a Afghanistan don makomar kasar.
Ma’aikatar tsaron Afghanistan ta ce hare-haren ta sama sun kashe mayakan Taliban 30 kuma ana gudanar da bincike kan ikirarin cewa har da farar hula a cikin wadanda aka kashe.
Facebook Forum