Fadan da aka yi tsakanin jami'an tsaron Afghanistan da mayakan Taliban a cikin sa'oi 24 da suka gabata ya yi sanadiyyar kisan mutane da dama a cewar rahotanni, ciki har da mayaka daga bangarorin biyu da kuma farar hula.
Har yanzu tashin hankalin da ake yi na zaman kalubale ga tattaunawar da aka dade ana jira wadda ake yi yanzu a Doha babban birnin Qatar, wadda ta hada da manyan wakilan da ke shawarwari daga bangaren ‘yan Taliban da gwamnatin Kabul.
Jami'an Amurka sun ce tattaunawar da ake yi tsakanin bangarorin biyu da ke fada a Afghanistan za ta maida hankali ne kan cimma "cikakkiyar yarjejeniyar tsagaita" da kuma kulla yarjejeniya a siyasance da nufin kawo karshen yakin da aka kwashe shekaru 40 ana yi a kasar da ke kudancin nahiyar Asiya.
Facebook Forum