PLATEAU, NIGERIA - Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa, DSP Ramhan Nansel, ya ce sun dauki matakin hana zanga-zangar ne don hana taho mu gama tsakanin magoya bayan jami'iyyu.
Matan, wadanda suka sanya bakaken tufafi wasu kuma suka fito tsirara, tun farko sun kai kokensu ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa a jihar Nasarawa.
Honarabul Stella Oboshi, shugabar jam'iyyar PDP a jihar Nasarawa, ta ce suna zanga-zangar ne da addu’ar Allah ya bi musu kadinsu na zabe.
Masanin shari'a a Najeriya Barista Yakubu Sale Bawa, ya ce shugaban jami'ar Jos Farfesa Tanko Ishaya wanda ya kasance jami'in da ya tattara kuri'u a jihar Nasarawa, ya gudanar da aikinsa bisa tsarin doka, sai dai wanda bai gamsu ba ya je kotu.
Dokar Najeriya dai ta ba 'yan kasa damar gudanar da zanga-zangar lumana amma hukumomi na iya dakatarwa in sun lura lamarin zai iya tada hankali da rasa rayuka da dukiyoyi.
Saurari cikakken rahoto daga Zainab Babaji: