Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Sandan Najeriya Sun Sanar Da Korar Wasu Jami’ai 3 Da Ke Kare Mawaki Dauda Kahutu Rarara


Rundunar yan sanda
Rundunar yan sanda

Kakakin Rundunar ‘yan sandan Najeriya CSP Muyiwa Adejobi, a cikin wata sanarwar da ya aike wa Muryar Amurka, ya ce an dauki matakin ne biyo bayan samunsu da laifukan da suka saba aiki.

Jami’an 'yan sandan da bidiyonsu ya karade shafukan sada zumunta, an gansu suna harba bindigogi da harsasan gaske a sama, yayin da suke wa mawakin rakiya.

Al’amarin wanda ya faru a kauyen Kahutu garin mawakin, a ranar 7 ga wannan watan na Afrilu ya janyo Allah wadai daga jama’a daga sassa dabam-daban a kasar.

Dauda Kahutu Rarara (Instagram/Kannywoodcelebrties)
Dauda Kahutu Rarara (Instagram/Kannywoodcelebrties)


Wannan ya sa rundunar ‘yan sandan ta kamo jami’an tare da kaddamar da bincike kan al’amarin, abinda ya sa bayan binciken aka same su da laifukan yin amfani da makami ba bisa ka’ida ba, da wasa da aiki, da rashin da’a, da kuma yin hasarar harsasai.

Jami’an da aka samu da laifin, wato Sufeta Dahiru Shayibu, Saja Abdulkshi Badamasi, da Saja Isa Danladi daga bisani an koresu daga aiki.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG