Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Rantsar Da Solomon Arase A Matsayin Shugaban Hukumar ‘Yan Sanda


Sabon Shugaban Hukumar
'Yan Sanda
Sabon Shugaban Hukumar 'Yan Sanda

A yau Laraba, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da tsohon shugaban ‘yan sanda Solomon Arase a matsayin shugaban hukumar ‘yan sanda na kasa.

Shugaba Buhari ya gabatar wa Majalisar sunan tsohon shugaban ‘yan sandan kamar yadda doka ta tanadar a sashin dokar Najeriya na 153 sakin layi na daya na kundin tsarin mulkin Najeriya.

An rantsar da sabon shugaban hukumar bayan kammala taron kaolin Najeriya wattani biyu bayan da Majalisar Dattijai ta tabbatar da shi.

Arase, wanda yayi aiki a matakai daban daban, ciki har da shugabantar sashin tattara bayanan manyan laifuka, sashen dake kula da tattara bayanai na hukumar ‘yan sandan Najeriya yayi ritaya a shekara ta 2016 bayan kammala wa’adin aikinsa a matsayi babban sufeton ‘yan sandan Najeriya.

Bayan Arase, shugaba Buhari ya rantsar da wasu mutane biyar a matsayin mambobin Hukumar kula da tabbatar da starin gwamnati wato CODE OF CONDUNCT BUREAU. An kuma yi wa tsohon Hafsat hafsoshin makeriya karkashin mulkin Sojan Janar Sani Abatcha, marigayi Laftanal Janar Oladipo Diya wanda ya rasu a ranar lahadi addu’a.

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG