To sai dai wani jigo a jam'yyar kuma tsohon kwamishana Dr. Danlami Arabs Rukuje ya yiwa 'yan jam'iyyarsu hannunka maisanda. Ya ce 'yan siyasa su sani cewa zamani goma sarki goma. Kowa da zamaninsa. Jam'iyya ce ta hadasu. Ya ce yadda 'yan PDP suka hada kai a lokacin Danjuma Goje har ya yi mulkin shekaru takwas haka ya kamata 'yan jam'iyyar su hada kansu. Yakamata su ba gwamnan yanzu hadin kai ya yi mulkinsa ya kare. Lokacin gwamna Goje ba'a taba jin an samu baraka cikin jam'iyyar ba. Ya ce abun da aka yi da a dora akai a cigaba da zaman tare domin jama'a su dinga zaben PDP.
An tambayeshi abun da yasa ana korafi yanzu. Ya ce kowa nada irin nasa mulkin. Idan kida ya sauya dole rawa ma ta canza. Gwamna Goje ya yi nashi mulkin ya tafi, kamata ya yi a bar gwamna Ibrahin Hassan Dankwanbo ya yi nashi ya gama. Amma idan kida ya canza mutum ya ce tashi rawar ba zata canza ba to rawarshi ma ba zata yi daidai da kidin ba.Ya ce ya ji mutane suna maganganu. Ba'a siyasa mutum daya. Kan shugabanci, Dr Rukuje ya ce idan mutum ya yi shugabaci ya sauka to ko ya tuna da wani abun da ya kamata ya fada bai fada ba to sai ya yi hakuri domin lokacinsa ya wuce.
Domin jam'iyyarsa ta cigaba da cin zabe ya ce 'yan jam'iyyar su yadda cewa akwai shugabanni a kowane mataki. Amma abun da yafi mahimmanaci shi ne mutunta juna. Sabili da haka a hadu a cigaba da yin aiki tare. Idan mutum ya yi kuskure lokacin da yake mulki to ya yi sai a manta da kuskuren.
Ga karin bayani n Sa'adatu Fawu.