Kwamitin da ya kunshi gwamnan Zamfara Yari da tsohon kakakin majalisar walikan Najeriya Alhaji Aminu Masari ya ziyarci Sokoto inda ya gana da 'yan jam'iyyar. Gwamnan Zamfara Alhaji Yari ya ce yayin da shugabannin jam'iyyarsu ta kasa suka ziyarci Sokoto a kokarinsu na san jawo gwamnonin PDP bakwai da suka buturewa jam'iyyarsu ta PDP zuwa tasu, 'yan jam'iyyar sun yi korafin ba'a bi ta kansu ba.
Gwamna Yari ya ce idan akwai wadanda ransu ya baci sabili da abun da ya faru uwar jam'iyya tana neman gafara. Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya ce idan an yiwa mutum laifi aka dawo neman gafara to sun yafe. Ya ce duk wani dan siyasa a Sokoto shi ya taba zama ubangidansa. Don haka idan yaron gida ya ce yana son ya dawo kuma ba tilasta masa aka yi ba, idan ya zo za'a duba a ga ko ya cancanta.
'Yan jam'iyyar sun ce bayan jam'iyyarsu ta kafu basa bukatan wasu bata gari da suka kira agwagi masu bata ruwqa.
Umar Faruk Sanyinna nada rahoto.