Tun da farko dai Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kebe ranakun Talata 26 da kuma Jumma’a 29 don gudanar da zabukan fidda ‘yan takarar Shugabannin Kananan Hukumomi da Kansiloli na jam’iyyar PDP mai mulkin jihar, in ji wakiliyarmu Zainab Babaji.
Zainab ta ce a wata takardar da gwamnatin Jos ta fitar mai dauke da sa hannun Sakataren Gwamnatin Jihar ta Filato Shaddrack Best, Gwamnatin ta ce bayan ta yi nazarin yanayin tsaro ne ta yanke shawarar jinkirta gudanar da zabukan a wadannan kananan hukumomin.
Wakiliyar ta mu ta kuma tattauna da wasu masu ruwa da tsaki a harkar siyasa ciki har da wani mai suna Dan Manjang, wanda ya ce shi bai ga dalilin jinkirta zabukan ba. Ya ce ana dimokaradiyya kuma sai gashi ana wani abu mai kama da munafurci saboda, a cewarsa, an sami zaman lafiya a Jos fiye ma da 2008, amma lokacin an yi zabe. To amma ya ce lallai akwai wasu kananan hukumomin da har yanzu babu zaman lafiya.
Shi kuwa wani mai suna Malam Muhammadu Yusuf Kanam, wanda wani jigon dan jam’iyyar adawa ne, ya ce au saboda irin dinbin kudaden da kananan hukumomin biyu ke samu daga gwamnatin tarayya aka dage zabensu don a yi ta facaka da su, au saboda wadanda su ka daga din na ganin za su fadi ne idan an yi zaben.