Farfasa Ango Abdullahi daya daga cikin wadanda suka halarci taron ya danganta halin da Najeriya ke ciki da matsalar rashin shugabancin nagari. Ya ce abun da mutum ya shuka shi zai girba. Ya ce abun dake faruwa yanzu su suka jawo shi., wato laifinsu ne. Sabo da haka su ne zasu taru su nemi maganinsa. Ya ce sun san abun dake faruwa don haka dole su san abun da zasu yi su fita a ciki. Ya ce shugabanci ne ya lalace kuma ya kamata su kawo gyara. Lalacewar shugabanci ke kawo lalacewar kasa. Ya ce ya zama wajibi arewa ta san abun da zata yi ta tabbatar an samu shugabanni na gari da zasu fitar da mutane daga irin bala'o'in da kasar ta shiga musamman arewa.
Sai dai 'yan rajin kare hakin talaka irin su Solomon Dalung ya ce rashin aikin yi da tabarbarewar ilimi na cikin abubuwan da suka kawo ma kasar matsaloli. Idan ana son samun masalaha to dole a tashi tsaye. Ya ce idan ba'a yi gyara ba to wata rana kasar zata kama wuta.Idan ko har ta kama wuta wadannan matasa da ba'a yi masu tanadi mai kyau ba kuma basu da komi da zasu rike to zasu saka kasar cikin rigingimun tashin hankali mara iyaka.
Alhaji Bashir Ahmad shugaban kungiyar ya ce lokaci ya yi da kungiyoyi zasu kawo nasu gudunmawar. Duk taron da aka yi da shawarwarin da aka cimma dole a mikasu ga shugabanni.idan za'a samu canjin da ake bukata.
Ibrahim Abdulaziz nada bayani.