Jam'iyyar PDP bangaren Bamanga Tukur, wato tsohuwar, ta zargi gwamnatin jihar, wato bangaren sabuwar da yi mata hawan kawara.Bangarorin biyu ne ke jayayya kan kujerar shugabancin karamar hukumar. A wajen taron manema labarai sakataren PDP bangaren Bamanga Tukur ko kuma tsohuwar PDP, Barrister A. T. Shehu wadanda suka rantsar da Mr. James Utenda a matsayin shugaban karamar hukumar bayan hukumcin wani kotu sun zargi gwamnatin jihar da yi masu hawan kawara. To amma tuni bangaren gwamnatin ta garzaya zuwa kotu domin daukaka kara.
Barrister A.T. Shehu ya ce babu wata doka da ta ba gwamna izinin rantsar da ko kansalo bama shugaban karamar hukuma ba. Ya ce rantsar da Mr. James Utenda na kan ka'ida.Ya ce sabon shugaban hukumar ya rubutawa duk wadanda suka cancanta ya rubutawa har da bankuna cewa ya kama aiki. To amma bangaren gwamnatin jihar sun zauna ofishin kakakin majalisar jihar sun yi kasafin kudin karamar hukumar. Daga baya kuma sun je sun jire kudin karamar hukumar.
A nata bayani gwamnatin jihar ta bakin kwamishanan kananan hukumomi Dr. Salihu Bakari Jire ta ce batun ba haka yake ba. Ya ce me yasa lauyansu zai rantsar da Mr. James Utenda. Me ya sa bai kawo takardar shaidar cewa ya ci zabe ba daga INEC? Har yanzu babu wani umurni daga kotu. Shi kuma Barrister abun da ya yi taka doka ne.
Al'ummar karamar hukumar suna kokawa kan rashin sani halartacen shugabansu.
Ibrahim Abdulaziz nada rahoto.