Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Niyyar Canja Samson Siasia In Ji NFF


Hukumaar kwallon kafa ta Najeriya, ta baiwa kocin Super Eagles Samson Siasia tabbacin cewa babu wani shiri na canja shi da wani Koch daga waje a halin yanzu.

Babban sakataren hukumar kwallon kafa ta Najeriya Mohammed Sanusi, wanda ya furta hakan yace ana bukatar Siasia ya doke kasar Egypt domin samun gurbi a kasar cin kofin nahiyar Afirka, kuma hukumar tayi amanna cewa zai kai labara.

Yace hukumar nada yakinin cewa Siasia zai cimma wannan burin, kuma za’a bashi duk goyon bayan da yake bukata domin kaiwa ga gaci.

Sakataren yana mai cewa hakikanin gaskiya basu san daga inda wannan maganar ta samo asali ban a cewa ana neman canja shi ba.

Bamu bukatar wani abinda zai daukewa ‘yan wasan mu hankalin daga abinda suka sa a gaba na doke kasar Misira, kuma muna da yakinin cewa Siasia, zai iya shi yasa aka doramasa alhakin horas da ‘yan wasan bayan da Sunday Oliseh, ya ajiye aiki.

Abinda muke bukata shi aduo’i da goyan baya daga ‘yan Najeriya.

XS
SM
MD
LG