Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya kaddamar da wasu jerin gidaje guda dari da Gidauniyar Muhammad Indimi ta soma ginawa a garin Bama domin taimakawa wadanda rikicin Boko Haram ya daidaita.
Garin Bama dai shine ya fi kowane gari shan wuya a hannun ‘yan Boko Haram saboda irin kone konen da suka yi a garin.
Gidauniyar ta kuduri gina gidaje dari dari a garuruwan Bama da Gamboru Ngala kuma ana sa ran gidauniyar zata kammala gidajen na Bama a watan Disamba na wannan shekara kana ta fara na Gamboru Ngala.
Gwamnan jihar ta Borno, Kashim Shettima yayi farin ciki tare da godewa Alhaji Muhammad Indimi akan wannan hobasar da ya yi.Gwamnan ya kara da cewa babu wanda ya taimaka masu a jihar Fiye da Alhaji Dangote da shi Muhammad Indimi. Ya kira masu hannu da shuni su taimaka. Yace ko a garin Bama akwai attajirai da yawa amma ko gina aji daya basu yi ba.
Shima da yake bayyana dalilin da yassa ya yanke kudurin gudanarda aikin,Alhaji Muhammad Indimi yace ‘Duk mutumin kirki in ya ga mutanensa na wahala ya kamata ya zo ya taimake su. ”
A Gamboru Ngala Muhammad Indimi yace zai gina gidaje 100 kowane da dakuna uku. Baicin gidajen, har ila yau zai gina musu dakin shan magani da makaranta tare da bada ruwa da wutar hasken rana.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.
Facebook Forum