Tun farko, karamin ministan man fetur na Najeriya Dr Ibe Kachukwu, ya zargi shugaban kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC, Dr. Maikanti Baru, da yin gaban kansa wajen ba da kwangiloli ba a kan ka’ida ba.
Haka kuma Dr Kachukwu ya zargi Dr Maikanti Baru, da raina shi saboda wai baya yi masa biyayya.
A martanin da ya mayar, Dr Maikanti ya ce duk abubuwan da ya yi, ya yisu ne da yawun fadar shugaban kasa ta Aso Rock, wato ba baskiya ba ne yayi gaban kansa.
A cikin wannan “ja ni, in ja ka” ne Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya fito fili ya bayyana abinda ya sani kan maganar. Ya ce shine ya baiwa Dr Maikanti Baru izinin kashe kudin lokacin da yake rike da shugabancin kasar yayinda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke Ingila wurin jinya. Haka kuma Osinbajo ya fayyace cewa kudaden na rance ne, ba kwangila ba.
To sai dai a fahimtar Dr Abubakar Umar Kari na Jami’ar Abuja, irin wannan cece-kucen na manyan jami’an gwamnati na raunana martabar gwamnatin a gaban jama’a da ma duniya gaba daya.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani
Facebook Forum