Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KENYA: Masana Na Ganin Matakin da Madugun ‘Yan Adawa Ya Dauka Na da Hadari


 Raila Odinga madugun 'yan adawana Kenya
Raila Odinga madugun 'yan adawana Kenya

Barrister Kassim Gana Gaidam, masanin harkokin zaben kasa da kasa, na ganin matakin da Raila Odinga, madugun ‘yan adawan kasar Kenya ya dauka na janyewa daga zabe mai zuwa na da hadari

Biyo bayan matakin da madugun 'yan adawar kasar Kenya, Raila Odinga ya dauka na janyewa daga takarar shugaban kasa da za a sake gudanarwa a watan da mu ke ciki, yanzu masana harkar zabe na kasa da kasa na ganin akwai abun dubawa.

Barrister Kassim Gana Gaidam, masanin harkar zabe na kasa da kasa wanda kuma wanda shine sabon kwamishinan hukumar zabe ta INEC a jihar Adamawa,, yace akwai hadari game da matakin da madugun adawar na Kenya ya dauka.

Shima dai wani masani, Abdullahi Prembe, yace akwai bukatar ‘yan siyasar Afrika su dauki darasi daga zaben shekarar 2015 da aka yi a Najeriya.

Hukumar zaben kasar Kenyar dai ta bayyana shugaban kasa mai ci a yanzu, Uhuru Kenyatta, a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da ya gabata, da kuri'a miliyan 1.4.

Tuni dai kotun kolin kasar ta yanke hukuncin cewa a ranar 26 ga wannan watan na Oktoba ne za’a sake zaben.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:25 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG