Cynthia Pettway, matashiya ‘yar makarantar sakandire ta gwamnati dake jihar Alabama a kasar Amurka, wadda take cikin matsanaciyar rashin lafiya, da hakan ya hanata halartar taron kammala makarantar, kasancewar tana gadon asibiti.
Hakan bai hana ta halartar taron ba, don kuwa mahaifiyarta ta sayo wata na’ura mai sarrafa kanta da ake kira “Robot” a turance, wanda ya wakilci dalibar tana gadon asibiti.
An kawata na’urar sanye da rigar makaranta dauke da na’ura a hannu mai hoton bidiyo “iPad”, inda yarinyar take zaune a gadon asibiti tana kallon duk abubuwa da ake gudanarwa a yayin bukin, kana mutane na ganin ta yayin da take zaune a bakin gadon asibiti.
Dalibar Cybthia, ta bayyana cewar wannan shine abun da yafi faranta mata rai a rayuwa, domin kuwa tana tunanin cewar ya za ayi bukin kammala makarantar ta ba tare da ita ba, amma tsarin da mahaifiyar ta tare da makarantar suka yi ya faranta mata rayuwa matuka.
Facebook Forum