Hukumar binciken sararrin samaniya ta Amurka da ake kira NASA a takaice, na shirin tura wani dan karamin jirgin sama mai saukar ungulu dake sarrafa kanshi zuwa duniyar Mars, a shirin kai ziyarar nazarin duniyar wadda yanayinta Ja ne da hukumar ke yi.
Ranar Jumma’ar da ta gabata hukumar ta sanar da cewa za ta tura jirgin mai sarrafa kanshi duniyar Mars a karkashin shirin binciken duniyar da ake kira Mars 2020 da turanci, wannan na zaman wata sabuwa fahasa da zata gwada karfin jirgin akan gudanar da bincike da kutsawa wuraren da ba a iya gani daga duniyar bil’adama.
A wani sansanin kere-keren hukumar NASA dake kudancin California aka kera Jirgin mai saukar ungulu.
Jirgin saman na da nauyin kilogram 1.8, gangar jikinsa kuma tana kwatankwacin girman ‘yar karamar kwallo, da kuma farfeloli da ke juyawa da saurin gaske- abu mai muhimmanci a yanayin duniyar ta Mars. Sinadarin hasken rana kuma za su iya caza batirin jirgin.
Za’a tsara umurnin da jirgin zai bi, saboda nisan dake tsakanin duniyar Mars da ta bil’adama ba zai bari a iya sarrafa jirgin ba daga duniyar bil’adama.
Facebook Forum