Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaddamar Morell Da Classiq: Mahangar Limamin Casu


Nazir Ahmed Hausawa
Nazir Ahmed Hausawa

A wannan zamanin dai kam babu yadda za’a yi ka kirga mawakan Hausa Hip Hop, biyar ba tare da sunan Morell ko Classiq ya fito ba; dukan su mawakan sun samu daukaka da farin jini a fadin Najeriya, da kasashen ketare. Ban cika son dora mawaka akan ma'auni ba, domin a fahimta ta kowa da irin baiwar da Allah ya yi masa.

Classiq Tare Da Morell
Classiq Tare Da Morell

Hausa Hip hop, dai an dade da fara shi a arewacin Najeriya, kuma matasa da dama sun fara cin albarkar wannan sana’a, daya daga cikin abubuwan da suka birgeni a cikin sana’ar shi ne babu hayaniyar wane ya fi wane kamar a sauran wurare, kusan a kowanne lokaci za ka ga yadda mawakan ke tallafawa juna ta hanyar tallata ayyukan sauran gami da girmamawa a shafukan sada zumunta.

A ranar 14 ga watan Mayu ne dai kwatsam! ina duba Instagram, sai na ga Morell, ya saki maimaicin tsohuwar wakarsa mai taken “Ba Wani Bugatti” inda ya yi aiki tare da Classiq, kuma a shafinsa na soundcloud, ya rubuta “This song supposed to drop last year so……” ma’ana “ya kamata a ce an saki wannan wakar a bara amma....”, a guje na garzaya domin sauraro na riga na san za ta yi wuta.

Wannan ba shi ne karo na farko da gwarazan mawakan suka yi aiki tare ba, a’a sun yi wakoki da dama, daya daga cikin ayyukansu da nake so shi ne wakar da Deezell, ya gayyace su ciki mai taken “Babu Ruwan Mu Da Haterz” tare da wasu mawakan da nake kauna irin su DJ. AB.

“Ba Wani Bugatti” (Remix) ta yi dadi domin kidan wakar ya ja hankalina sosai ba zan iya kwatanta shi da na farko ba, sannan yadda mawakan suka zuba rap, abin ba’a cewa komai sai dai "mixing," din wakar ya yi hayaniya da yawa, (ta iya yiwuwa lasifika ta ce.) Kar dai in cika ku da surutu, kwatsam! sai na ga Classiq ya yi post, a shafinsa na Instagram.

@Classiq
@Classiq

Abin da Classic ya fada a cikin post dinsa shi ne; “Ina mai alfaharin yin aiki da wannan waka “Ba Wani Bughatti” amma dan uwa na yi mamaki da kuma rashin jin dadin ka aiko min da wani kida daban a farko shekarar 2016, yanzu kuma ka saki wakar da wani kida daban ba tare da sanina ba….Hmmm.

Ina tunanin a mutunce da kuma irin alakar da ke tsakaninmu gami da kwarewar aiki ya kamata a ce an sanar da mu sauye sauyen da aka yi da dalilan yin su. Amma Allah ya san komai, Allah ya albarkaci nemanka Babban Yaya….Allah ya sa albarka da karin daukaka a cikin abinda kake yi #AllahYaTaimakiSarkiMusa AreWaMaFia”.

Ai ina ganin wannan post sai jikina ya yi sanyi na fara tambayar kaina me ke faruwa? Kafin kace kwabo masoya sun yi ca akan wannan post daga bangarorin duka biyu, masoyan Classiq na kare shi yayin da masoyan Morell, ke ganin wanna ba batun da za’a yi shi a bude bane. Ina gab da in tuntube su kai tsaye kasancewar su kannena duka su biyun sai Morell, ya yi nashi post din a Instagram kamar haka.

  • @Morell
    @Morell
  • morellakilahIn the late hours of today, a member of my team got an email of an open letter from @classiq I followed the story to Classiq's page & I've seen all that's been said so far. I want to openly say that I have no motive & I didn't approve the release of the song at first. It was leaked by my producer & friend @braceofspades who reworked on the remix and tweaked the instrumental. He had the data of the song & was enthusiastic about dropping it because of the magnitude of the project.
    I wasn’t planning on releasing the song in the first place cos somehow i felt its kinda too late to drop a remix of Bawani Bugatti that was originally released in 2015 in 2018. All the same I take the blame & I want to say to my brother barnabas Buba (classiq) & his team that I am deeply sorry. I respect your craft & I would never do a thing to damage what uve built from hard work.
    Arewa rap is on the rise & The Almighty knows I wouldn't do anything to spoil the culture. For the fans please it's a #NordanOrtty x #ArewaMafia collabo so no need to argue or take sides just enjoy the music and spread love only❤️. #Nagode!!! Ps : I actually think we did well bro!! The fans love it"
  • Abin da Morell ke cewa shi ne:
  • “Da yammacin jiya ne daya daga cikin abokan aikina ya turo min budaddiyar wasika daga Classiq, inda na bi kanun abin da ke faruwa a shafinsa kuma ya zuwa yanzu na ga duk abin da aka fada.

“Ina so in fada a bayyane cewa banda wata manufa kuma ban ba da umurnin sakin wannan waka tun farko ba, Producer, na kuma abokina @braceofspades, shi ya yi sauye-sauye a kidan ya kuma kwarmata wakar, yana da bayanan wakar kuma yana da yakinin sakin wakar sakamakon girman da take dashi."

"Ban yi niyyar sakin wannan waka ba da farko saboda na yi tunanin ta tsufa an yi wakar Bugati, ta farko a shekarar 2015, me zai sa in sake ta a shekarar 2018. Duk da haka na dauki laifin kuma ina son in baiwa dan uwana Barnabas Buba (Classic) da tawagarsa hakuri. Ina mutunta aikinka ba zan taba yin wani abu da zai kawo nakasa kan aikin da muka gina da wahala ba."

"Yanzu Rap, a arewa ya fara tasowa kuma Allah ya sani bazan yi wani abu don lalata al’adar ba. Ga masoya kuwa #NordanOrtty x #ArewaMafia baki daya babu bukatar kumfar baki ko wariya, mu ji dadin wakokin mu, mu yada kauna kadai. #Nagode!! Kuma a ganina mun yi kokari dan'uwa!! Masoya sun so wakar.”

Bayan naga wannan post sai na ce to babu wani dalili da zai sa in yi kundumbala cikin wannan magana.

Amma duk da haka, ina son jan hankalin masoyan wakokin Hausa Hip hop, da idan ba za mu fadi alkhairi ba to mu yi shiru. Kowa na da abin da yake so amma hakan ba zai sa mu rika iza wuta in an batawa masoyanmu rai ba. Ya kamata mu sani cewa kowannen mu na da ‘yancin bayyana ra’ayinsa kuma bayyana ra’ayi ya fi ayi ta kunbiya kunbiya ko kuma munafunce munafunce.

Ga kannena kuwa, Classiq da Morell: Classiq banga laifinka da zabin yadda ka bayyana ra’ayinka ba. Morell, ka burgeni kwarai da kaci girma ka baiwa Classiq, hakuri haka ake so, kirana a gareku shine muna kallon ku, Allah ya dora muku wani girma da ko kuna so ko bakwaso duk abinda kuka yi yana da tasiri a cikin matasa saboda haka a rika cizawa ana hurawa watarana sai labari. Allah ya bamu sa’a.

Limamin Casu kuma Babban Yaya Ziriums.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG