Kamfanin Instagram zai yi ma manhajar sa garanbawul, a inda zai kayatar da ita da wani sabon tsari da zai rika bayyana ma mutane adaddin lokacin da suka kashe a shafin a duk lokacin da suka shiga cikin manhajar don kallo da saka hotuna ko labarai.
Wannan matakin da kamfanin instagram ke shirin dauka wanda Mr. Kevin Systrom ke shugabanta, na zaman wani bangaren kokarin da kamfanonin fasahar ke yi na sa mutane su rage yawan amfani da wayoyin su.
Ana sa ran sabon tsarin mai take “Usage insights” a turance zai rika nuna ma mutane adaddin mintoci da suka kashe a shafin a kowace rana. Kana kuma mutun zai iya ganin adadin mintuna da ya yi a cikin shafin na tsawon watanni.
Mr. Systrom, ya yarda da cewar yawan lokaci da mutane ke kashewa a kan shafukan yanar gizo ka iya zama babbar matsalace ga rayuwar su, abin da yasa kamfanonin fasaha kamar su instagram fara daukar mataki akan lamarin.
Facebook Forum