Wasu daga cikin manyan kamfanoni masu kera motoci a yankin kasashen turai na wani hadin gwuiwa wajen ganin sun fadada kasuwar motoci masu aiki da hasken rana ko batiri, inda suke ganin akwai bukatar kamfanonin su gina wasu tashoshin cajin batiri akan manya manyan hanyoyi.
Hikimar yin hakan zai saukaka ma mutane damar cajin motocin su cikin sauki, batare da bata lokaci ba, ganin wasu lokutta mutane kan tsaya na tsawon lokaci don jiran batirin su ya cika kamin su kama hanya.
Sabon tsarin zai samar da tashohi akan hanyoyi daga kasar Norway, zuwa kudancin kasar Italiya har zuwa kasar Portugal da Poland. Hakan dai na nuna cewar akwai jan aiki a gaban kamfanonin da suka hada da kamfanin BMW, Ford da Volkswagen.
Wannan wani yunkuri ne na ganin an inganta motocin wannan zamanin masu shigowa kasuwa, don ganin ana samar da motoci da zasu rage dogaro da man fetur. Kamfanonin sun dau alwashin, shekara mai zuwa duk wata mota da zasu kera zata zama mai amfani da batiri ne.
Ganin yadda kamfanin kasar Amurka na Tesla, ke cin karenshi babu babbaka a duniyar motoci masu amfani da batiri, ya kamata suma sauran kamfanonin su shiga sahu.
Facebook Forum