WASHINGTON D.C —
Wata Mata ta bude wuta da bindiga a babban ofishin kamfanin “You Tube” dake a kusa da garin San Francisco a jiya Talata, inda ta raunata mutane uku kafin ta kashe kanta.
‘Yan sandan San Bruno, sun gano wadda ta yi harbin mai suna Nasim Najafi Aghdam, ‘Yar shekaru 39, yar garin San Diego.
“Har zuwa yanzu haka dai babu wata shaida da zata nuna wadda ta yi harbin ta san wadanda ta harba ko kuma su ta yi niyyar harbewa,” a cewar sanarwar da ‘yan sandan suka bayar.
Rahotanni sun ce Aghdam, ta zargi Kamfanin You Tube da cewa suna toshe hanyar watsa fayafayanta na bidiyo da kuma kassara hanyoyin samun kudinta. Kamfanin na You Tube dai har yanzu bai ce komai akan wannan lamari ba.
Facebook Forum