Wani dan adawa siyasar kasar Kenya yace hukumomin kasar sun bugar dashi ne suka kwashe shi da karfin tsiya zuwa Dubai.
Miguna, ya fada a wani sako a shafin sa na Facebook cewa an tsare shi a ban daki a babban filin jirgin saman Nairobi tun ranar litinin bayan ya dawo daga kasar Canada inda aka maida shi a watan jiya.
Miguna ya ce hukumomin sun balle ban dakin a yau Alhamis suka yi masa allura da wani abu sannan suka ja shi da karfin tsiya zuwa cikin wani jirgin saman pasinja na kampafanin Emirates.
Lauyoyin Miguna sun ce an fitar da shi daga kasar duk da cewa kotu ta bada umarnin a sake shi. Wata babbar kotu a ranar laraba ta bayyana cewa raini ne kin bin dokar odar ministan cikin gida da shugaban ‘yan sanda suka yi.
Shi dai Miguna zuwa an dauke shi daga Kenya, aka maida shi kasar Canada, a watan da ya wuce bayan ya rantsar da shugaban ‘yan adawa Raila Odinga a wani bikin wasa na rantsar da shugaban kasa a watan Janairu don nuna rashin goyon bayan sa na sake zaben Shugaba Uhuru Kenyatta. An kwace wa Miguna, fasfo kafin a sashi ya bar kasar da karfin tsiya, duk da cewa yana da fasfo din kasar Kenya, koda yake yana tafiye-tafiyen sa da fasfo din kasar ta Canada.
Facebook Forum