Kimanin watannin hudu ke nan da suka gabata, da mota kirar kamfanin Tesla, mai tuka kanta tayi hadari, a yanzu kuma sai ga wata sabuwar mota mai tuka kanta ta sake samu hadari. A cewar kamfanin Tesla, wannan hadarin ya abkune biyo bayan fasinja dake cikin motar bai rike sitiyari ba cikin dakikoki 6 kamin abkuwar hadarin.
Kamfani ya kara da cewar dama dokar itace a duk lokacin da mutun yake cikin irin wannan motar, akan bukaci mutu da ya dinga lura da yadda motar take tafiya, kana a duk lokacin da mutun ya kai ga kwana zai rike sitiyarin don ganin an gujema hadari.
Fasinjan dake cikin motar wani matashi ne mai shekaru 38, Walter Huang, injiniya a kamfanin Apple, ya mutu a sanadiyar abkuwar hadarin, kamfanin ya bayyanar da jajen shi ga iyalin mamacin, kanfanin na aiki da hukumar bincike ta gwamnatin tarayya don ganin an ganon sanadiyyar abukuwar hadarin.
Motar nada hankalin rage gudu a duk lokacin da hakan ya bukatu, kana tana iya canza hannu da duk wasu abubuwa da suka kamata, hakan ya karasa kamfanin tunanin sababbin hanyoyi da zai inganta motocin shi masu tuka kansu.
Facebook Forum