Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Gwauruwa Ta Dauki Nauyin Kudin Makarantar Masu Koyon Aikin Magani A New York


Ruth Gottesman
Ruth Gottesman

Makarantar koyon aikin likita a birnin New York za ta zama kyauta ga duk ɗalibai daga yanzu saboda gudummawar dala biliyan 1 daga wata tsohuwar farfesa, gwauruwar wani mai saka hannun jari na Berkshire Hathaway.

Lokacin da mijin Ruth Gottesman mai shekaru 96 ya mutu a cikin 2022, ya bar wani abu da ya ba matarsa mamaki, dala biliyan 1 a hannun jari na kamfanin hanayen jarin Berkshire Hathaway.

Gottesman ta gaya wa New York Times. cewa, umarnin mijinta kawai shine, "Ki yi duk abin da ki ga ya dace da shi,

David Gottesman
David Gottesman

Da farko dai, Gottesman ta kasa yanke shawarar abin da za ti da wannan makudan kudade, amma bayan ‘ya’yanta sun shawarce ta da kada ta dauki lokaci mai tsawo kafin ta yanke shawara, sai ta yanke shawarar ba da gudummawar kuɗdn gaba daya ga Kwalejin Magunguna ta Albert Einstein da ke Bronx, da unguwa mafi talauci a birnin New York, in ji jaridar New York Times.

"Ina so in tallafa wa dalibai a Einstein domin su sami kuɗin koyarwa kyauta," in ji ta.

Makarantar ta ce za a mayarwa dukkan daliban da ke shekarar karatu ta hudu a halin yanzu kudin da suka biya na karatunsu na bazara na 2024, kuma daga watan Agusta, duk daliban makarantar na yanzu da wadanda za a dauka gaba za su samu yin karatu kyauta.

Gottesman ta ba da sanarwar ga daliban na yanzu da kanta a safiyar Litinin. Da zaran kalmar “karatu kwauta” ta fito daga bakinta, daliban da ke dakin taron suka fashe da ihu, suna tafawa da tsalle daga kan kujerunsu, wasu na kuka, kamar yadda aka nuna a wani faifan bidiyo daga reshen asibitin makarantar, Montefiore Health System.

Gottesman, farfesa mai koyarwa a fannin likitan yara a Einstein, ta fara aikinta a kwaleji a 1968, a cewar sanarwar manema labarai na makarantar. Ta kasance shugabar kwamitin amintattu na makarantar, mukamin da ta rike tun daga shekarar 2007 zuwa 2014.

Kudin koyarwa na shekara guda a makarantar ya haura dala 59,000, wanda hakan ya sa yawancin daliban da suka kammala karatun su ke cin bashin fiye da dala 200,000, kafin su kallama makaranta kamar yadda binciken mujallar Times ya nuna.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG