Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Shida Sun Jikkata A Harbin Jirgin Kasa a New York


jirgin karkashin kasa a birnin New York
jirgin karkashin kasa a birnin New York

Ma’aikatan kashe gobara sun ce mutane shida sun jikkata, kuma  mutum daya daga cikinsu  na  cikin mawuyacin hali sakamakon harbin da aka yi a tashar jirgin karkashin kasa a birnin New York da yammacin jiya Litinin.

Hukumar kashe gobara ta ce an sanar da hukumomi da misalin karfe 4:30 na yamma (agogon GMT 2130) game da harin, kuma tuni aka kai marar lafiya daya da ke cikin mawuyacin hali zuwa asibiti, kamar yadda ma’aikatar kashe gobara ta bayyana. Ba a bayar da dalilin yin harbin ba.

Hare-hare kan jama'a sun zama ruwan dare a Amurka, inda ake da bindigogin da suka fi jama’a yawa kuma kusan kashi uku na Amurkawa manya sun mallaki bindiga.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG