Wanda ya assasa makarantar, Barrister Zannan Mustapha ya gaya ma wakilinmu Haruna Dauda Biu cewa daga kudaden shigar da ya ke samu daga wasu gidajen kifi uku da yah aka. Ya ce da kudin da ake samu daga sayar da kifayen ake samun kudaden ciyarwa da tufatarwa da sauran bukatar dalibai marayu.
Umar Garba wani dalibin makarantar ne da ya ce ya yi shekaru biyar a makarantar. Ya tabbatar ma wakilinmu cewa makarantar ce ke daukar komai dinsa kamar yadda wani dalibi ma mai suna Abubakar Mustapha ya tabbatar. Haka zalika wasu daliban makarantar sun sami makarantu na gaba a wasu wurare. Barrister Zannan Mustapha ya ce tashe-tashen hankulan da ke faruwa a yankin arewa maso gabashin Nijeriya sun haifar da marayu da dama ta yadda cikin shekaru biyu da su ka gabata an sami marayu dubu da dari biyar (1,500).