Tsohon gwamnan jihar Kano kuma dań takarar shugaban Najeriya karkashin inuwar jam’iyyar NNPP, sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa ya kai ziyara birnin Owo na jihar Ondo da wasu ‘yan bindiği suka aikata ta’adi ne don tattaunawa da masu ruwa da tsaki da suka hada da gwamnatin jihar, sarakunan gargajiya, da sauran masu ruwa da tsaki don a zauna da juna lafiya.
Kwamkwaso ya bayyana hakan ne a yayin hira ta musamman da muryar Amurka ya na mai cewa idan abubuwa marasa dadi irin wannan suka faru, dole ne zarge-zarge da abubuwa marasa dadi zasu biyo baya tsakanin wadanda suke ‘yan wannan gari da kuma mutane da suke baki a wannan guri.
A cewar Kwankwaso bayan samun wasu abubuwa da suka faru mara dadi sakamakon wannan hari, ya ga ya dace ya kai ziyara don tattauna da masu ruwa da tsaki a yanki don a ba wa juna hakuri a zauna lafiya.
Haka kuma Kwankwaso ya kai ziyara zuwa mujami’a da al’ummar da kuma sarakunan gargajiyar yankin da lamarın ya auku don nuna godiya ga yadda suda dauki al’amarin da kariya da suka ba wa ‘yan arewa mazauna garin kamar yadda wasu mutanen arewa suka shaida ma sa.
Kwankwaso ya kuma gana tare da tattauna da sarakunan hausawa a yankin tare da jawo hankalinsu da cewar su ci gaba da yin abubuwa na zaman lafiya a inda suke zaune, su hana yaran arewa shaye-shaye da sauran abubuwa mara dadi su kuma bada mahimmanci ga sa yaransu a makaranta inda kowa ya yi alkawarin a zauna lafiya daga bisani.
A cewar Kwankwaso, dole ne a bar hukuma ta yi aikinta don gano wadanda suka aikata wannan aika-aika a kuma hukunta su diaidai da dokar kasa.
A bangaren tsaida mataimakinsa a takarar zaben shekarar 2023 mai karatowa, Kwankwaso ya ce jam’iyyarsa ta NNPP ta kafa kwamitin da ya tantance duk masu niyyar zama mataimakinsa kuma an tsaida wani a masayin mataki na wucin Gadi la’akari da yadda hukumar Zabe mai zaman kanta ta Najeriya wato INEC ta bada alawus na jam’iyyu su tsaida mata imaka tare da damar canjawa cikin kwanaki 40 bayan mika suna a wa’adin farko da ita hukumar zaben ta sanya.
A ranar 6 ga watan Yunin da muke ciki da wasu yan bindiga da ba'a san ko su wanene ba suka dasa abubuwa masu fashewa a wata mujam'iar a birnin Owo na jihar Ondo inda aka rasa rayuka sama da 40.
A saurari karin bayani cikin sauti: