Shugaban daukacin mambobin Katolika a Najeriya, Henry Yunkwap a taron manema labarai da yayi a Jos, fadar Jahar Filato, ya bayyana rashin jin dadinsa da yadda aka kashe wadanda basu ji ba basu gani ba, yayinda suke gudanar da ibada a ranar Lahadi.
Haka ma a wata sanarwa, shugaban darikar ECWA ta kasa da kasa, Rabaran Stephen Panya-Baba wanda ya nuna damuwarsa kan yadda kashe-kashe ke neman zama jiki a Najeriya, ya bukaci hukumomi su gudanar da kyakkyawan bincike kan kisan na masu ibada a Owo.
Rabaran Panya-Baba yace Najeriya dake da mabambantan addinai da kabilu, dole tayi duk mai yiwuwa wajen hana wargajewar al’ummar ta.
Shugaban na ECWA ya kuma bukaci kirista su dukufa ga addu’o’i yayinda ya roki gwamnati ta karfafa matakan tsaro a kasar.
Ita ma kungiyar gwamnonin Arewa, a wata sanarwa da sanya hannun shugabanta kuma gwamnan Jahar Filato, Simon Lalong tace kisan ya nuna karara yadda bata gari ke neman haddasa gaba da kiyayya a tsakanin mabiya addinai a Najeriya.
Kungiyar gwamnonin ta kuma bukaci jami’an tsaro su kamo wadanda suka kashe masu ibadan da masu goya musu baya, don su fuskanci hukunci da zai zamo izina ga sauran masu aikata barna da haddasa rikici a Najeriya.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: