Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane Bakwai A Wasu Kauyukan Jihar Filato


‘Yan Bindiga Sun Kai Hari, Suka Hallaka Mutane Bakwai A Wasu Kauyukan Jihar Filato
‘Yan Bindiga Sun Kai Hari, Suka Hallaka Mutane Bakwai A Wasu Kauyukan Jihar Filato

Gwamnatin Jihar Filato ta umurci hukumomin tsaro a Jihar da su yi duk mai yiwuwa wajen gano wadanda ke barazana ga rayukan al’ummar Jihar, musamman a kauyukan karamar hukumar Bokkos.

PLATEAU, NIGERIA - Gwamnan Jihar, Simon Lalong ya bada umurnin ne bayan wasu munanan hare-hare da ‘yan bindiga su ka kai kauyen Kuliyas a karamar hukumar Bokkos, suka hallaka mutane bakwai, ciki har da basaraken yankin.

Kansila mai wakiltar Butura a karamar hukumar Bokkos inda lamarin ya auku, Isaac Mafuyas Julson ya ce mutane bakwai ne ‘yan bindigar suka halaka a kauyuka biyu, suka kuma kona gidaje goma sha daya.

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari, Suka Hallaka Mutane Bakwai A Wasu Kauyukan Jihar Filato
‘Yan Bindiga Sun Kai Hari, Suka Hallaka Mutane Bakwai A Wasu Kauyukan Jihar Filato

Shugaban karamar hukumar Bokkos, Joseph Gulwa ya bukaci mutanen yankin da su kai zuciya nesa, kar su dauki doka a hannunsu.

Kwamishinan Ilimi mai zurfi na Jihar Filato, Farfesa Bernard Matur ya ce gwamnati zata dauki mataki kan lamarin.

Rundunonin tsaro a Jihar da suka hada da ‘yan sanda, Soji, Civil Difens da Operation Rainbow sun ce sun dukufa wajen bincike don gano batagarin.

Saurari cikakken rahoton daga Zainab Babaji:

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari, Suka Hallaka Mutane Bakwai A Wasu Kauyukan Jihar Filato .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG