Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

TARABA STATE: An Hallaka Wasu Shugabannin Al'umma


Wani dansanda ke sintiri kan hanyar inda aka aikata ta'asar
Wani dansanda ke sintiri kan hanyar inda aka aikata ta'asar

Rikicin kailanci da na addini na neman zama ruwan dare gama gari a jihar Taraba inda wasu sun yaudari wasu shugabanin al'umm daga bisani suka hallakasu.

Bayanai sun nuna cewa wasu suka kira shugabannin al'umma da cewa su je su sasanta Fulani da kabilar Mumuye dake rikici da junansu.

To amma daga baya sai gawarwakin shugabannin aka samu an daddatsasu. Lamarin ya kusa ya jawo wani sabon tashin hankali.

Wadanda aka kashe sun hada da dagacin Yanya Alhaji Musa Kacalla da kuma wani mai anguwa Malam Adamu Jahun.

Dan Adamu mai anguwa Musa yace wasu mutane ne suka gayyacesu da su je su sasanta wasu Fulani da manoma Mumuye dake fada da junansu suna barna a jeji..

Lamarin ya sa dagacin da mai anuguwa suka tashi suka nufi jejin. Babu wanda ya san abun da ya biyo baya saidai an samu gawarwakinsu da aka daddatse a jejin.

Wani aminin dagacin yace suna cikin alhini kuma abun da suke bukata daga mahukunta shi ne su kama mutanen da suka gayyacesu tunda an sansu.

Kisan dauki daidai yana yawan faruwa a jihar ta Taraba cikin 'yan kwanakin nan.

An kira mahukunta da su yi gaggawa su kama wadanda suke da hannu cikin wannan kisan saboda a samu zaman lafiya domin basarake aka kashe da mai anuguwarsa..

Hukumar 'yansanda tace tana bincike kuma zata kamo wadanda suke da hannun a ta'asar.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:30 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG