Shugaban Amurka Donald Trump da uwargidansa Melania, za su kai ziyarar jaje ga iyalan mutane 11 da aka kashe a makon da ya gabata, a wani wurin ibadar Yahudawa a birnin Pittsburgh da ke jihar Pennsylvania.
Sai dai wasu shugabannin Yahudawa na yin kira ga Trump da ya dakatar da ziyarar ta shi, har sai ya yi watsi da akidarsa da fifita fararen fata.
A jiya Litinin Fadar Gwamnatin Amurka ta White House ta sanar da ziyarar, inda ta bayyana cewa shugaba Trump da mai dakinsa za su kai je birnin na Pittsburgh mai dumbin tarihi.
Maksudin ziyarar a cewar Fadar ta White shi ne, su nuna goyon baya ga Amurkawa tare da jajintawa al’umar yankin da abin ya shafa.
Wannan ziyarar ta Trump na zuwa ne a daidai lokacin da mambobin wurin ibadar da aka kai harin, wanda ake kira Tree of Life Synagogue suke gudanar da jana’izar farko ga mamatan.
Daga cikin mamatan har da wasu 'yan uwa biyu, David Rosenthal mai shekaru 54 da dan uwansa Cecil mai shekaru 59.
A wata hira da ya yi da gidan talbijin na CNN, Magajin Garin birnin na Pittsburg, Bill Peduto, shi ma ya bai wa shugaba Trump shawara da ya dage ziyarar ta sa.
Ziyarar a cewar Peduto za ta kara dora nauyi akan ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro wadanda hankulansu suka karkata wajen samar da tsaro a wurin taron jana’izar da ake yi.
Shugabannin wata kungiya mai fafutukar ganin ci gaban Yahudawa, su ma sun nemi shugaba Trump da ya dakatar da ziyarar, amma Limamin wurin Ibadar na Tree of Life, Jeffery Myers, ya ce suna lale marhabin da zuwan shugaban birnin na Pittsburgh.
Facebook Forum