WASHINGTON, DC —
Gwamnatin jihar Adamawa,tayi tir da harin da aka kai garin Mubi, ta kuma yi alkawarin taimakawa wadanda suka jirkata da kuma wadanda suka rasa dukiyoyisu.
Darakata yada labarai na gwamna jihar ne ya furta haka, ya kuma yi kira ga jama;a,duk inda aka mota ko jaka wanda ba’a san abunda yake ciki ba a sanar da jami’an tsaro.
Ya kuma yi kira da akai rahoton duk wata mota ko jaka da aka da ake zargi ga jami'an tsaro domin kare lafiyar juna.
Yayin da al’amura suka fara kwantawa a Mubi bayan tashin bom,rahotani na nuna cewa kawo yanzu addadin wadanda suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka samu munanan raunuka na karuwa.
Kamar yanda mazauna garin na Mubi ke cewa addadin wadanda suka rasa rayukansu yafi wanda hukumomi suka bada.
Hare-haren ‘yan bindiga na karuwa cikin kwanakin nan a jihar Adamawa, masammam a yankunan Madagali, dake makwabtaka da jihar Borno.