Wasu jami'an tsaro da mazauna garin sun ce an jefa bam din ne a kusa da wani filin kwallon kafa dake kusa da wata makarantar firamare dake da cunkoson jama'a.
Ganau sun ce an kwashi gawarwakin mutane da dama. Gaf da kammala kwallon lokacin da mutane ke tafiya sun kawo wani wuri inda akwa shaguna da masu sayar da kayan lambu da kayan toye-toye sai kwatsam bam ya tashi. Lokacin da abun ya faru kusan magariba ne domin haka babu wanda ya san iyakan mutanen da suka rasa rayukansu. Sabili da lokacin hana fita ya karato kowa na kokarin komawa gida kafin karfe bakwai da dokar zata fara aiki.
Abun mamaki jim kadan bayan sojoji sun isa wurin sun zagaya sun kuma tafi sai bam din ya tashi. Bam din ya rutsa da yara da matasa da mata da yawa.
Rundunar 'yansandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin amma tace bata da adadin wadanda suka rasa rayukansu ko suka jikata. Yanzu dai 'yansandan suna bincike kuma zasu sanar wa jama'a cikakken bayanai.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.