Ijabula Seltimari yace lokacin da 'yan Boko Haram suka kawo hari a garin Izghe da misalin karfe tara na dare shi yana kwance a daki sai suka buga kafar dakinsa da gaya masa cewa idan bai bude ba zasu fasa kofar da bindiga domin sun zo ne su kasheshi.
Yana bude kofar dakinsa sai suka tambayeshi takardar motarsa da na babur da ya saya. Duk ya kwasa ya basu. Kana suka sake tambayar abun da yake dashi sabili da haka duk kudaden dake hannusa nashi da na wasu ya basu. Amma sai da suka sakawa motarsa wuta.
Bayan sun kwace kudadan dake hannunsa sai suka sa ya kwanta kasa. Mutane da suka fito, yayansa da kakansa da matar yayansa rike da jinjiri da makwaftansa duk suka harbe har lahira.
Duk da harbin da suka yiwa Ijabula sau biyu Allah ya rayar dashi amma gefen jikinsa daga hannun dama ya mutu. Yace baya jin komi. Ya godewa Allah da ya bashi rai sai dai yanzu abun da zasu ci shi ne matsala.
Ga rahoton Ibrahim Alfa.