Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Zanga-Zangar End SARS Sun Cancanci Yabo - Minista Sunday Dare


Sunday Dare, Mnistan Matassa Da Wasanni Na Najeriya
Sunday Dare, Mnistan Matassa Da Wasanni Na Najeriya

Yayin da gwamnatin Najeriya ke ci gaba da yin Allah wadai da lalata dukiyar jama’a da matasa masu adawa da cin zarafin da ‘yan sanda ke yi wa jama’a, wani ministan kasar na kallon lamarin ta fuska dabam.

Ministan matasa da wasannin Najeriya Sunday Dare, ya fadi cewa matasan sun cancanci a jinjina musu saboda za a samu sakamako mai kyau a kasar. Ko da ya ke, ya ce mamayar da bata gari suka yi a zanga-zangar da ta kai ga asarar dukiyar al’uma abin takaici ne.

A wata hira da Grace Alheri Abdu ta yi da shi kwanan nan, ministan ya ce matasan Najeriya sun falka daga barci, sun tashi tsaye wajen neman ganin an inganta fannin ‘yan sanda, an samar da shugabanci na gari, an kuma kawo karshen yadda ake kallon matasan Najeriya a matsayin masu iya aikata laifi. Ministan ya ce lallai bai kamata a yi wa matasan Najeriya wannan kallon ba, ba tare da wani nazari ba.

“Bai kamata kawai a dauki matashin Najeriya a matsayin dan dafarar yanar gizo ba ko kuma idan ka na dauke da kwamfutar tafi-da-gidanka hakan na nufin ba halattacciyar sana’a ka ke yi ba, an dade ana hakan kuma saboda abubuwa da yawa da suka faru, da kashe-kashe ba bisa ka’ida ba, cin zali, azabtarwa, kuntatawa, cin hanci, ina gani su suka sa ‘yan Najeriya suka ce sun gaji,’ a cewar Dare.

Zanga Zangar EndSARS a Abuja 4
Zanga Zangar EndSARS a Abuja 4

Ya kara da cewa, a madadin al'ummar Najeriya, saboda baya ga matasan sauran wasu ‘yan kasar sun fuskanci lamarin, a ganinsa shi ya sa matasan suka tattaru suka shirya zanga-zangar, suka kuma gabatar da korafe-korafensu. Sun isar da sakonsu ga gwamnati, a na ta bangaren gwamnati ta maida martini akan kari.

Bukatoci guda biyar ne matasan suka gabatar wa gwamnati, kuma gwamnati ta amsa. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ‘yan kwanakin kadan bayan gabatar da korafe-korafen ya yi wa ‘yan kasa jawabi, ya umurci dukkan matakan gwamnati su biya wadannan bukatun guda biyar. Wasun su nan take aka aiwatar da su wasu kuma an kafa kwamitoci kuma ana ci gaba da gudanar da bincike a duk fadin kasar.

A ranar 8 ga watan Oktoban shekarar 2020 ne dai matasa suka dunguma kan tituna a sassan Najeriya dabam-daban don nuna rashin jin dadinsu akan yadda rundunar ‘yan sandan SARS mai yaki da ‘yan fashi da makami a Najeriya ke gallaza wa jama’a tare da neman a soke rundunar, zanga-zangar da ta rikide ta koma tarzoma a wasu wuraren. Yanzu dai kowa ya zuba ido ya ga sauye-sauyen da za a yi nan gaba don kawar da aukuwar duk wani mummunan lamari irin wannan nan gaba.

XS
SM
MD
LG