Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Mutane Da Ake Kira ‘Yan Ansaru Masu Kama Da Boko Haram Sun Bayyana A Jihar Kaduna


Gwamna El Rufai (Facebook/El Rufai)
Gwamna El Rufai (Facebook/El Rufai)

A daidai lokacin da al'umomi a wasu sassan Jihar Kaduna ke fama da hare-haren 'yan-bindiga da sace-sacen mutane don neman kudin fansa, wasu al'umma a yankin karamar hukumar Birnin Gwari sun ce akwai wasu mutane da ake kira 'yan-Ansaru dake yawan zuwa garuruwan su dauke da manyan makamai.

KADUNA, NIGERIA - Yankunan Kuyello, Kwasa-kwasa, Unguwan Gwandu, Unguwan Makera da Shado na cikin garuruwan da wadannan mutane da al'ummar yankin su ka ce sun yi kama da 'yan Boko Haram na yawan zuwa.

Daya daga cikin al'ummar yankin da ya nemi a sakaya sunan shi, ya ce duk da manyan makamai wadannan mutane da akan kira su 'yan-Ansaru su ke dauke da su, basa cutar da al'umma.

Duk da rashin cutarwa daga wannan kungiya da ake kira Ansaru, masana harkokin tsaro na ganin akwai hadari cikin zama da su, a cewar Manjo Yahaya Shinko mai ritaya.

Dama dai an taba samun irin wannan kungiya a yankin Jihar Naija can a baya, kuma ko kwanan nan ma rahotannin na ganin irin wannan kungiya a wasu yankunan karamar hukumar Igabi abun da ya sa wasu ke ganin ya kamata gwamnati ta zauna da su don sanin manufofinsu kada daga baya abun ya gagari kundila.

Saurari rahoto cikin sauti daga Isah Lawal Ikara:

Wasu Mutane Da Ake Kira ‘Yan Ansaru Masu Kama Da Boko Haram Sun Bayyana A Jihar Kaduna
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG