Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Obama Ya Bukaci 'Yan Majalisa Su Zartas Da Kudirin Dokar Samar Da Ayyukan Yi


Majalisar Dokokin Amurka
Majalisar Dokokin Amurka

Shugaba Obama ya ce 'yan jam’iyyar Republican a majalisun dokoki ba sa maida hankali akan matsalar tattalin arzikin Amurka

Shugaba Barack Obama yace sabon rahoton dake cewa attajirai na kara kudancewa a yayin da masu dan karfi ke ci gaba da fama, ya nuna cewa wakilan jam’iyyar Republican a majalisun dokoki ba sa mayar da hankali akan matsalar tattalin arzikin Amurka.

A cikin jawabin shi na sati-sati Mr.Obama ya fada cewa a yayin da ake karfafawa jama’a guiwar neman arziki da samun nasara a rayuwa, kuma sai ga shi a Amurka masu karbar babban albashi kawai ne ke samun karin arziki.

Mr.Obama yace shawarar shi da ya gabatar game da samar da ayyukan yi ta bukaci yin karin haraji ga mutanen da ke karbar albashin da ya wuce dola miliyan daya a shekara a lokaci guda kuma a yi ragin haraji ga masu dan karfi da kananan ‘yan kasuwa.

Yace kodayake a can baya ‘yan Republican sun goyi bayan irin wannan shawara, yanzu kuma sai ga shi, sun zo suna sa siyasa a cikin al’amarin.

kakakin majalisar wakilan Amurka John Boehner na jam'iyyar Republican a yayin wata tattaunawa da manema labarai akan kasafin kudin Amurka da kuma maganar samar da ayyukan yi a kasar
kakakin majalisar wakilan Amurka John Boehner na jam'iyyar Republican a yayin wata tattaunawa da manema labarai akan kasafin kudin Amurka da kuma maganar samar da ayyukan yi a kasar

Amma da yake mayar da martani a cikin jawabin ‘yan Republican na sati-sati, dan majalisar dokoki Bobby Schilling mai wakiltar jahar Illinois ya fada cewa ba siyasa ce za ta farfado da tattalinn arzikin Amurka ba. Yayi kira ga shugaba Obama da ya umarci ‘yan Democrat din majalisar dattabai su amince da shawarar da ‘yan Republican su ka gabatar game da samar ayyukan yi a Amurka.

Schilling ya ce shirin jam'iyyar Republican na samar da ayyukan yi a Amurka zai kirkiro da ayyukan yi ta hanyar rage haraji. Kuma yace shirin zai canza tsarin biyan haraji, ya toshe duk wata kafar taka doka sannan kuma ya taimakawa kasar ta biya bashin da ke kan ta.


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG