Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nakasassu Na Fuskantar Matsaloli a Nijar


Wani mai nakasa
Wani mai nakasa

Kiran da hukumomin Nijar ke yi na cewa a daina bara nakasassu sun ce sun bi umurnin gwamnati sun koyi sana'a wasunsu har makaranta suka je sun kuma yi watsi da bara amma har yanzu babu taimakon da gwamnati ta basu

A koyaushe hukumomin Nijar na kiran nakasassu su daina bara su koyi sana'a su daina mayar da bara sana'a.

Duk da kiran na gwamnati nakasassun sun ce har yanzu basu gani a kasa ba. Suna sarafa kayayyaki da dama saboda da horaswar da suka samu amma ba'a sayen kayansu.

Nakasassun na kera abubuwa da dama amma gwamnati bata taba basu kwangilar kera wani abu ba ko a matsayin tallafi.

Nakasassun na kera abubuwa da dama. Suna dinki. Suna saka kujeru ta makafi. Suna aikin katako da na fata. Suna makanikanci. Babban burin nakasassun shi ne su ga 'yanuwansu nakasassu sun bar bara sun shiga sana'a.

Sun kira gwamnati ta rika basu aiki domin su dogara da kansu.

Madam Sani Aishatu direkta a ma'aikatar gwamnati, tace ta kan hadasu da NGOS domin samun taimako. Haka kuma gwamnati ta dauki nakasassu aiki kamar makafi zuwa aiki a wasu wurar.

Ga rahoton Tamar Abari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG