Batun hare hare a jihar ta Kaduna ya sa wasu kungiyoyi sun soma korafi kan yadda suka ce gwamnati ke laku-laku wajen ganin an kawo karshen tashin tashinar.
A wani taron manema labaru da wata kungiya mai radun neman kawo canji a jihar babban abun damuwar tasu shi ne halin ko in kula da gwamnatin jihar ke nunawa kan hare-haren da kuma wadanda hare-haren ke rutsawa da su. Hajiya Hafsat Muhammed Baba babbar jami'ar kungiyar tace kullum safiya zaka ji labarin da bashi da dadi. Ana kashe mutane. Mata an barsu ba mazansu yara kuma sun zama marayun karfi da yaji. Amma abun da ya fi damunsu shi ne yada aka bar yaran da matan kara zube babu wani kulawa daga gwamnati. Tace saboda haka basa jin dadin yadda ake gudanar da gwamnati.
Hajiya ta kara da cewa jama'a ana kashesu barkatai daga baya kuma a ce an kafa kwamitoci ko kungiyoyi. Su kuwa kwamitin basu iya dakatar da kashe mutane ba. Tace idan ana son a kawo karshen wannan abu dole shugabanci ya yi tafiya da adalci. Shugabanci kuma dole ya bude kunne ya ji koke-koken jama'a. Shugabanci na bukatar idan abun farin ciki ya samu al'umma a je a nuna farin ciki da su. Idan kuma abun bakin ciki ya faru a je a jajatan masu. Tace ko shugaba Obama lokacin da aka kashe yara ya bar aikinsa ya tafi ya jajantawa mutanen da abun ya shafa.
Amma babban daraktan yada labaru na gwamnatin jihar Alhaji Ahmed Abdullahi Maiyaki yace soke zuwa taron neman zaman lafiya a duniya da ake yi a kasar Amurka da gwamnan ya yi babbar hujja ce da ta nuna ya damu matuka. Yana kan hanya da ya ji abun da ya faru ya dawo domin ya duba ya ga abun da ya farud da kuma daukar matakin da ya kamata domin kawo karshen wannan ta'asar.
Ga karin bayani.