Wadannan 'yan bindiga da aka ce sun tafi a jerin gwanon babura masu yawan gaske, sun shafe sa'o'i da yawa su na kai farmaki a kan mutanen garuruwa irinsu Marabar Maigona, Unguwar Rimi, Layin Galadima da 'Yar Doka da Maidaura.
Wani mazaunin garin Marabar Maigona, Ibrahim Ahmadu, yace mutanen sun zo a kan babura suka kewaye garin baki daya, suka rutsa da kowa a ciki su na sara da harbin mutane.
Amma rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta musanta cewa an kashe mutane da yawa haka. Kakakin rundunar, DSP Aminu Abubakar Sadiq, yace yawancin 'yan jarida su na magana ne da wadanda ba su ga abubuwan da suka faru da idanunsu ba, sai wadanda suka ji labari kawai.
Yace babu wanda aka kama, amma ana gudanar da bincike, a bayan da ;'yan bindigar suka gudu zuwa cikin daji.
A garin Argungu a Jihar Kebbi ma, wasu 'yan bindiga su hudu a kan babura sun kai farmaki, suka yi sanadin mutuwar mutane 3, cikinsu har da dan bindiga guda, da dan sanda daya da kuma wani farar hula.
Kakakin 'yan sandan Kebbi, Sufritanda Mohammed D. Mainagge, yace an samu nasarar kama biyu daga cikin wadannan 'yan bindigar da aka ce 'yan fashi ne.