Wakilin Muryar Amurka a Maiduguri yayi bayanin yadda mutane da sanduna da adduna suka rika yin kukar kura su na abkawa kan 'yan bindigar dake dauke da muggan makamai, inda aka ce da yawa daga cikin mayakan tilas suka juya baya da gudu a saboda sarkin yawa da aka yi musu.
Jiragen saman yaki na sojoji sun rika bi su na sako bama-bamai a kan 'yan bindigar dake neman tserewa, yayin da 'Yan Gora suka yi ta kama wasu su na mika su ga jami'an tsaro.
Akwai rahotannin dake cewa 'yan bindigar sun samu shiga barikin Giwa suka kubutar da wasu daga cikin wadanda ake tsare da su, amma ba a samu tabbacin hakan daga hukuma ba, haka kuma ba a samu ta bakin wani wanda ya ce ya ga hakan da idanunsa ba.
Jiragen yaki na ci gaba da shawagi, yayin da jama'a suka fara leko kofar gidajensu don yi ma juna barkar kubuta tare da tattauna wannan harin ba zata.
Ga bayanin da wani mazaunin unguwar Bolori a Maiduguri yayi mana kan yadda 'yan bindigar suka shigo da irin abubuwan da suka wakana har zuwa lokacin Sallar jumma'a a yau.