Ranar Juma'a da ta gabata aka kai hare-hare a wasu kauyuka uku a Karamar Hukumar Kaura lamarin da ya kai ga zaman zullumi a yankin. Ko da safiyar Lahadi mutane sun sha guje-guje a Sabon Tasha domin wani harin. Kuma cikin daren Lahadin an kai wani sabon hari a masarautar Kataf.
Kungiyar al'ummar kudancin jihar Kaduna SUKAFO a takaice, ta cewa idan ana son a samu zaman lafiya a yankin kudancin jihar to wajibi ne manya-manyan jami'an tsaron jihar su tare kawai a yankin.
A wani shiya an ce gidaje kusan dari aka kone tare da dabbobi da sauran dukiya. Mutane sama da dubu biyar suka tsira amma sun rasa muhallansu. Cikin Fulani maharan da aka kashe biyu an haifesu ne a garin Manchok. Mai magana da yawun 'yan kudancin Kaduna yace idan gwamnati bata dauki mataki ba to su zasu dauki nasu matakin domin ba zasu bari ana yanakasu kamar kaji ba.
Duk da jam'an tsaron da aka ce an sa bukata bata biya ba domin maharan suna shiga su kashesu su kuma fita lafiya. Yace ya zama wajibi su tashi tsaye. Filanin dake kai masu hari suna cikin daji ne. A nemesu a kawar dasu. Jami'an tsaro su hau tsaunuka inda Fulanin ke fakewa su zakulo su.
Amma daya daga cikin shugabannin Fulani a kudancin Kaduna ya musanta batun cewa akwai hannun Filani a harin sai dai ya tabbatar da harin ranar Lahadi. Yace Filanin da aka kashen irin masu wucewa ne. Babu wani Filani mazaunin Kataf da aka kashe ko kuma yake da hannu a harin. Yace tun shekarar 2011 ake kashe Filani saidai su basu iya kuka ba ne duniya ta ji. Kan yadda za'a samu maslaha yace kowa a bashi hakinsa. Yace Filani suna yankin yau fiye da shekaru dari biyu.
Ga karin bayani.