Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutanen Gaza Sun Koma 'Shan Ruwan Lambatu' - Hukumar WHO


A Palestinian woman bakes bread as children sit next to her, while Gaza residents face crisis levels of hunger and soaring malnutrition, in Khan Younis in the southern Gaza Strip, Jan. 24, 2024.
A Palestinian woman bakes bread as children sit next to her, while Gaza residents face crisis levels of hunger and soaring malnutrition, in Khan Younis in the southern Gaza Strip, Jan. 24, 2024.

A yanzu haka wasu mutanen Gaza sun koma shan ruwan lambatu mai najasa da kuma cin abincin dabbobi, a cewar Hanan Balkhy, darektan yankin gabas ta tsakiya ta Hukumar Lafiya ta Duniya tana mai rokon a kara kai dauki cikin gaggawa zuwa yankin da aka yi wa kawanya.

Darektan ta yi gargadin cewa yakin da ke tsakanin Isra'ila da Hamas ya yi tasiri kan harkokin kiwon lafiya a fadin yankin.

A cikin Gaza, "akwai mutanen da a yanzu suke cin abincin dabbobi, suna cin ciyawa, suna shan ruwan najasa, yayin da manyan motocin agaji ke tsare a wajen Rafah." masaniyar lafiyar yaran ta shaida wa AFP a wata hira da aka yi da ita a hedkwatar WHO da ke Geneva.

Palestinians crowded together as they wait for food distribution in Rafah, southern Gaza Strip, Nov. 8, 2023.
Palestinians crowded together as they wait for food distribution in Rafah, southern Gaza Strip, Nov. 8, 2023.

Majalisar Dinkin Duniya ta dade tana gargadin cewa yunwa na kara kunno kai a Gaza, inda mutane miliyan 1.1 kusan rabin al'ummar kasar ke fuskantar bala'i na karancin abinci.

Bayan ziyarar baya-bayan nan da ta kai mashigar Rafah daga Masar zuwa kudancin zirin Gaza wata muhimmiyar mashigar agaji da sojojin Isra'ila suka rufe a farkon watan da ya gabata, ta bukaci Isra'ila da ta "bude wadannan iyakokin".

Balkhy ta jaddada matsananciyar bukatun marasa lafiya a Gaza, tare da kusan mutane 11,000 masu fama da matsananciyar rashin lafiya da kuma wadanda suka samu raunuka da ke bukatar jinya.

Balkhy ta ce yakin ya yi mummunar illa ga matakan kiwon lafiyar jama'a, kamar ruwa mai tsabta, abinci mai kyau da rigakafi na yau da kullun, wanda ya haifar da kamuwa da cutar kyanda, gudawa da cututtukan numfashi.

"Zai yi tasiri sosai kan lafiyar kwakwalwa. Zai haifar da manyan cututtuka na damuwa bayan tashin hankali," ta yi gargadin.

Yakin Gaza mafi muni ya samo asali ne sakamakon harin da kungiyar Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 1,194, galibi mata da yara, a cewar wani alkaluman hukumomin Isra'ila.

Harin ramuwar gayya da Isra'ila ta kai a Gaza ya kashe mutane akalla 36,550, wadanda kuma akasarinsu mata da yara ne, a cewar ma'aikatar lafiya ta yankin Hamas.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG